📖 Mattiyu 28
-
1
¶ Da daddare ranar Asabaci, rana ta fari ga mako ta fara gabatowa, Maryamu Magadaliya da daya Maryamun suka zo don su ziyarci kabarin.
-
2
Sai aka yi girgizar kasa mai karfi, saboda mala'ikan Ubangiji ya sauko daga sama ya kuma murgine dutsen ya zauna a kai.
-
3
Kamanninsa kamar walkiya, tufafinsa kuma fari fat kamar suno.
-
4
Masu tsaron suka razana don tsoro suka zama kamar matattun mutane.
-
5
Mala'ikan ya yi wa matan magana cewa, “Kada ku ji tsoro, nasan kuna neman Yesu wanda aka gicciye.
-
6
Baya nan, amma ya tashi kamar yadda ya fada. Ku zo ku ga wurin da aka kwantar da shi.
-
7
Ku hanzarta ku gaya wa almajiransa, 'Ya tashi daga matattu. Duba, ya tafi Galili, can zaku same shi.' Gashi ni kuwa na fada maku.”
-
8
Matan suka yi hanzari suka bar kabarin da tsoro da murna, suka ruga domin su sanar wa almajiransa.
-
9
Sai ga Yesu ya tare su, yace masu, “A gaishe ku.” Sai matan suka kama kafar sa, suka kuma yi masa sujada.
-
10
Sai Yesu yace masu, “Kada ku ji tsoro. Ku je ku fada wa 'yan'uwana su je Galili. Can zasu ganni.”
-
11
Sa'adda matan suke tafiya, sai wadansu masu tsaro suka shiga gari suka fada wa Shugabanin Firistoci dukan abin da ya faru.
-
12
Firistocin suka hadu da dattawa suka tattauna al'amarin, sai suka bada kudi masu yawa ga sojojin
-
13
Sukace masu, “Ku gaya wa sauran cewa, “Almajiran Yesu sun zo da daddare sun sace gangar jikinsa lokacin da muke barci.”
-
14
Idan wannan rahoto ya isa wurin gwamna, za mu lallashe shi mu ja hankalinsa mu raba ku da damuwa.”
-
15
Sai sojojin suka karbi kudin suka yi abinda aka umarcesu. Wannan rahoto ya bazu a tsakanin Yahudawa, ya ci gaba har zuwa yau.
-
16
Amma almajiran sha daya suka tafi Galili, kan dutsen da Yesu ya umarcesu.
-
17
Da suka gan shi, suka yi masa sujada, amma wadansu suka yi shakka.
-
18
Yesu ya zo wurin su ya yi masu magana, yace, “Dukan iko dake sama da kasa an ba ni.
-
19
Sai kuje ku almajirantar da dukan al'ummai. Kuna yi masu baftisma cikin sunan Uba da na Da da na Ruhu Mai Tsarki.
-
20
Ku koya masu su kiyaye dukan abin da na umarce ku. Duba, ni kuma kullum ina tare da ku har karshen zamani.”