1¶ Sai kuma ya sake tafiya cikin Majami'a sai ga wani Mutum mai shanyayyen hannu.
2Wadansu mutane suna kallonsa sosai, su gani ko zai warkar da shi a ranar Asabar. don su zarge shi.
3Yesu ya ce wa mai shanyayyen hanun “ Ka tashi ka tsaya a tsakiyar kowa.”
4Sai ya ce wa mutane, “Ya dace a yi abu mai kyau aranar Asabar ko a yi mugunta; a ceci rai, ko a yi kisa? “Amma suka yi shiru.
5Sai ya dube su cikin fushi, yana bakin ciki da taurin zuciyar su, ya ce wa mutumin ka mikar da hanunka, sai ya mikar da hanunsa Yesu kuwa ya warkar da shi.
6Sai Farisiyawa suka fita da sauri zuwa wurin mutanen Hirudus suka shirya yadda za su kashe shi.
7Sai Yesu da almajiransa, suka tafi bakin teku. sai mutane dayawa suka bi shi, daga Galili da Yahudiya
8Daga Urushalima da Edom gaba da Urdun da kewayan Taya da Sidon, da baban taro, ya ji abinda yake yi. suka zo wurinsa.
9Ya tambayi almajiransa su shirya masa karamin jirgin ruwa domin yawan mutane, domin kada su murkushe shi.
10Ya warkar da mutane da yawa, yadda duk wadanda suke da cuttutuka suna kokari su taba shi.
11Duk sa'adda kazaman ruhohin suka ganshi, sai su durkusa a gabansa su yi ihu da karfi su ce, kai Dan Allah ne.”
12Ya umarce su da karfi kada su sa a san shi.
13Ya hau saman dutsen, ya kira wadanda yake bukar su, su zo wurinsa.
14Ya zabi guda goma sha biyu (ya kira su manzanni). Wadanda zasu kasance tare da shi, ya kuma aike su, su yi wa, azi,