📖 Ibraniyawa 3
-
1
¶ Don haka yanuwana tsarkaka, a bokan kira a samaniya. Yi la'akari da Yesu. wato Manzo da babban firist na shaidar bangaskiyarmu.
-
2
Shi amintacce ne na Allah, wanda ya bashi hidima, kamar yadda Musa ya kasance amintacce a gidan Allah.
-
3
Gama Yesu ya cancanci daukaka mafi girma fiye da ta Musa. Domin wanda ya gina gida, ya fi gidan nan daukaka.
-
4
Gama kowane gida, akwai wanda ya gina shi, amma mai ginin komai shine Allah.
-
5
Musa hakika amintaccen bawa ne a gidan Allah, yana ba da shaidar abubuwan da za su faru a nan gaba.
-
6
Amma Almasihu shi Da ne mai mulki a gidan Allah. Mu ne gidansa idan mun rike begenmu da dukkan zuciyarmu.
-
7
Saboda haka, kamar yadda Ruhu Mai Tsarki ya fadi: ''Yau, Idan kun ji muryarsa,
-
8
kada ku taurare zuciyarku kamar yadda 'ya'yan isra'ila suka yi cikin tawaye a lokacin gwaji a jeji.
-
9
A lokacin nan ne kakanninku suka yi mani tawaye, ta wurin gwada ni, bayan shekara arba'in suna ganin ayyukana.
-
10
Saboda haka na yi bakin ciki da wannan tsarar, sai na ce,' Kullum suna yawan bijirewa a zukatansu. Basu san tafarkuna ba.'
-
11
Don haka na yi rantsuwa a cikin fushina, ba za su shiga cikin hutuna ba.”
-
12
Ku yi hankali 'yan'uwa kada a tarar da mummunar zuciya marar bangaskiya a tsakaninku, zuciya wadda ke juyawa daga Allah mai rai.
-
13
Maimakon haka, ku karfafa juna a kowacce rana, muddun muna cikin wannan rana kada wani cikinku ya taurare zuciyarsa saboda yaudarar zunubi.
-
14
Gama mun zama abokan aiki da Almasihu, idan mun rike begenmu cikinsa da karfi, daga farko zuwa karshe.
-
15
Game da wannan, an fadi “Yau idan kun saurari muryarsa, kada ku taurare zuciyarku, kamar a kwanakin tawaye nan.”
-
16
Su wanene suka ji muryar Allah suka yi tawaye? Ba wadanda Musa ya yi masu jagora daga Masar ba ne?
-
17
Kuma da su wa Allah ya yi fushi shekara arba'in? Ba da wadanda suka yi zunubi ba ne, wadanda gawawwakinsu suka warwatsu a jeji?
-
18
Da su wa Allah ya rantse ba za su shiga hutunsa ba? In ba wadanda suka yi masa rashin biyayya ba?
-
19
Mun kuma gani cewa basu iya shiga hutunsa ba saboda rashin bangaskiyarsu.