📖 1 Yohanna 1
-
1
¶ Abin nan da yake tun daga farko, wanda muka ji, wanda muka gani da idanunmu, wanda muka gani hannuwanmu suka kama, a wajen maganar rai.
-
2
Ran kuwa aka baiyyana shi, muka gani, muka bada shaida, muka gaya maku labarin rai na har abada, wanda da yake a wurin Uba, aka kuma sanar da mu.
-
3
Wannan da muka gani muka ji muka baku labari, domin kuyi zumunci da mu, zumuncinmu kuwa tare da Uba yake da Dansa Yesu Almasihu.
-
4
Haka nan, muna rubuta maku wadannan abubuwa domin farin cikinmu ya cika.
-
5
Wannan shi ne sakon da muka ji daga wurinsa mu kuwa muka sanar da ku: Allah haske ne a wurinsa kuwa babu duhu ko kadan.
-
6
Idan mun ce muna zumunci da shi kuma muna tafiya cikin duhu, muna yin karya kuma bama aikata gaskiya.
-
7
Amma idan muna tafiya cikin haske kamar yadda yake cikin haske, muna zumunci da juna, jinin Yesu Dansa ya wankemu daga dukka zunubi.
-
8
Idan mun ce bamu da zunubi, muna rudin kanmu kenan, ba kuma gaskiya a cikinmu.
-
9
Amma idan mun fadi zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci da zai gafarta mana zunubanmu, ya kuma wankemu daga dukkan rashin adalci.
-
10
Idan mun ce bamu yi zunubi ba, mun mai da shi makaryaci kenan, maganarsa kuma bata cikinmu.