1Ku roƙi Ubangiji yă ba ku ruwa a lokacin bazara; Ubangiji ne yake yin gizagizan hadari. Shi ne yake ba wa mutane yayyafin ruwan sama yana kuma ba da tsire-tsire na fili ga kowa.
3“Ina fushi da makiyayan, zan kuma hukunta shugabannin; gama Ubangiji Maɗaukaki zai lura da garkensa, wato, gidan Yahuda, zai kuma sa su zama kamar doki mai fariya cikin yaƙi.
4Daga Yahuda dutsen kusurwa zai fito, daga gare shi za a samu abin kafa tenti, daga gare shi za a sami bakan yaƙi, daga gare shi za a sami kowane mai mulki.
5Tare za su zama kamar mutane masu ƙarfi suna tattake lakar tituna a cikin yaƙi. Domin Ubangiji yana tare da su, za su yi faɗa su kuma yi nasara a kan masu yaƙi a kan dawakai.
6“Zan ƙarfafa gidan Yahuda in kuma ceci gidan Yusuf. Zan maido da su domin ina jin tausayinsu. Za su zama kamar ban taɓa ƙinsu ba, gama ni ne Ubangiji Allahnsu zan kuma amsa musu.
7Mutanen Efraim za su zama kamar mutane masu ƙarfi, zukatansu kuwa za su yi murna kamar sun sha ruwan inabi. ’Ya’yansu za su gani su yi murna; zuciyarsu za tă yi farin ciki a cikin Ubangiji.
8Zan ba da alama in kuma tattara su. Ba shakka zan fanshe su; za su yi yawa kamar yadda suke a dā.
9Ko da yake na warwatsa su cikin mutane, duk da haka a can ƙasashe masu nisa za su tuna da ni. Su da ’ya’yansu za su rayu, za su kuwa komo.
10Zan komo da su daga Masar in kuma tattara su daga Assuriya. Zan kawo su Gileyad da Lebanon, har wuri yă kāsa musu.
11Za su ratsa cikin tekun wahala; zan kwantar da raƙuman teku dukan zurfafan Nilu kuma za su bushe. Za a ƙasƙantar da Assuriya, sandar sarautar Masar kuma za tă rabu da ita.
12Zan ƙarfafa su a cikin Ubangiji kuma a cikin sunansa za su yi tafiya,” in ji Ubangiji.