📖 Zabura 99
-
1
Ubangiji yana mulki, bari al’ummai su yi rawan jiki; yana zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, bari duniya ta girgiza.
-
2
Ubangiji mai girma yana a Sihiyona; an ɗaukaka shi a bisa dukan al’ummai.
-
3
Bari mu yabi girmanka da sunanka mai banrazana, shi mai tsarki ne.
-
4
Sarki mai iko ne, yana ƙaunar adalci ka kafa gaskiya; a cikin Yaƙub ka yi abin da yake mai adalci da kuma daidai.
-
5
Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu ku kuma yi masa sujada a wurin sa ƙafafunsa; shi mai tsarki ne.
-
6
Musa da Haruna suna cikin firistocinsa, Sama’ila yana cikin waɗanda suka kira bisa sunansa; sun kira ga Ubangiji ya kuwa amsa musu.
-
7
Ya yi magana da su daga ginshiƙin girgije; ya kiyaye farillansa da ƙa’idodin da ya ba su.
-
8
Ya Ubangiji Allahnmu, ka amsa musu; ka kasance wa Isra’ila Allah mai gafartawa, ko da yake ka hukunta ayyukansu marasa kyau.
-
9
Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu ku kuma yi sujada a dutsensa mai tsarki, gama Ubangiji Allahnmu mai tsarki ne.