📖 Zabura 98
-
1
Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, gama ya yi abubuwa masu banmamaki; hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki sun yi masa aikin ceto.
-
2
Ubangiji ya sanar da cetonsa ya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai.
-
3
Ya tuna da ƙaunarsa da kuma amincinsa ga gidan Isra’ila; dukan iyakar duniya sun ga ceton Allahnmu.
-
4
Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya, ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi;
-
5
ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya, da garaya da ƙarar rerawa,
-
6
tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago, ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki.
-
7
Bari teku su yi ruri, da kuma kome da yake cikinsa, duniya da kuma kome da yake cikinta.
-
8
Bari koguna su tafa hannuwansu, bari duwatsu su rera tare don farin ciki;
-
9
bari su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa domin yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya da adalci mutane kuma cikin gaskiya.