📖 Zabura 97
-
1
Ubangiji yana mulki, bari duniya tă yi murna; bari tsibirai masu nesa su yi farin ciki.
-
2
Gizagizai da baƙin duhu sun kewaye shi; adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinsa.
-
3
Wuta tana tafiya a gabansa tana kuma cinye maƙiyansa a kowane gefe.
-
4
Walƙiyarsa ta haskaka duniya; duniya ta gani ta kuma yi rawar jiki.
-
5
Duwatsu sun narke kamar kakin zuma a gaban Ubangiji, a gaban Ubangijin dukan duniya.
-
6
Sammai sun yi shelar adalcinsa, dukan mutane kuma suka ga ɗaukakarsa.
-
7
Dukan waɗanda suke bauta wa siffofi sun sha kunya, waɗanda suke fariya da gumaka, ku yi masa sujada, dukanku alloli!
-
8
Sihiyona ta ji ta kuma yi farin ciki kuma dukan ƙauyukan Yahuda suna murna saboda hukunce-hukuncenka, ya Ubangiji.
-
9
Gama kai, ya Ubangiji, kai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya; ana darjanta ka fiye da dukan alloli.
-
10
Bari masu ƙaunar Ubangiji su ƙi mugunta, gama yana tsaron rayukan amintattunsa yana kuma kuɓutar da su daga hannun mugaye.
-
11
An haskaka haske a kan masu adalci da kuma farin ciki a kan masu gaskiya a zuciya.
-
12
Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji, ku da kuke masu adalci, ku kuma yabi sunansa mai tsarki.