📖 Zabura 94
-
1
Ya Ubangiji, Allahn da yake ramuwa, Ya Allah wanda yake ramuwa, ka haskaka.
-
2
Ka tashi, ya Alƙalin duniya; ka sāka wa masu girman kai abin da ya dace da su.
-
3
Har yaushe mugaye, ya Ubangiji har yaushe mugaye za su yi ta murna?
-
4
Suna ta yin maganganun fariya; dukan masu aikata mugunta sun cika da fariya.
-
5
Suna murƙushe mutanenka, ya Ubangiji; suna danne gādonka.
-
6
Suna kashe gwauraye da kuma baƙi; suna kisan marayu.
-
7
Suna ce, “ Ubangiji ba ya gani; Allah na Yaƙub bai kula ba.”
-
8
Ku mai da hankali, ku marasa azanci a cikin mutane; ku wawaye, yaushe za ku zama masu hikima?
-
9
Shi da ya sa kunne ba don a ji ba ne? Shi da ya yi ido ba don yă gani ba ne?
-
10
Shi da yake yi wa al’ummai horo ba ya hukunci ne? Shi da yake koya wa mutum ba shi da sani ne?
-
11
Ubangiji ya san tunanin mutum; ya san cewa tunaninsu banza ne.
-
12
Mai albarka ne mutumin da ka yi masa horo, ya Ubangiji, mutumin da ka koyar daga dokarka;
-
13
kana ba shi sauƙi a lokacin wahala, sai har an haƙa rami wa mugaye.
-
14
Gama Ubangiji ba zai ƙi mutanensa ba; ba zai taɓa yashe gādonsa ba.
-
15
Za a sāke kafa hukunci a kan adalci, kuma dukan masu adalci a zuciya za su bi shi.
-
16
Wane ne zai yi gāba da mugaye domina? Wane ne zai ɗauki matsayi ya yi gāba da masu aikata mugunta domina?
-
17
Da ba don Ubangiji ya yi mini taimako ba, da tuni na zauna shiru a wurin mutuwa.
-
18
Sa’ad da na ce, “Ƙafata na santsi,” ƙaunarka, ya Ubangiji, ta riƙe ni.
-
19
Sa’ad da alhini ya yi yawa a cikina, ta’aziyyarka ta kawo farin ciki wa raina.
-
20
Zai yiwu kursiyin da ya cika da lalaci yă haɗa kai da kai, wanda yake kawo azaba ta wurin abin da ya zartar?
-
21
Sun yi ƙungiya tare a kan mai adalci suka yanke wa marar laifi hukuncin mutuwa.
-
22
Amma Ubangiji ya zama kagarata, Allahna kuma dutsen da nake samun mafaka.
-
23
Zai sāka musu saboda zunubansu yă kuma hallaka su saboda muguntarsu; Ubangiji Allahnmu zai hallaka su.