📖 Zabura 92
-
1
Yana da kyau a yabi Ubangiji a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,
-
2
don a yi shelar ƙaunarka da safe amincinka kuma da dare,
-
3
da kiɗin molo mai tsirkiya goma da kuma ƙarar garaya.
-
4
Gama ka sa na yi murna ta wurin ayyukanka, ya Ubangiji; na rera don farin ciki saboda ayyukan hannuwanka.
-
5
Ina misalin ayyukanka, ya Ubangiji, tunaninka da zurfi suke ƙwarai!
-
6
Mutum marar azanci ba zai sani ba, wawa ba zai gane ba,
-
7
cewa ko da yake mugaye suna girma kamar ciyawa kuma dukan masu aikata mugunta suna haɓaka, za a hallaka su har abada.
-
8
Amma kai, ya Ubangiji, za a ɗaukaka har abada.
-
9
Gama tabbatacce abokan gābanka, ya Ubangiji, tabbatacce abokan gābanka za su hallaka; za a watsar da dukan masu aikata mugunta.
-
10
Ka ɗaukaka ƙahona kamar na ɓauna; an zubo mai masu kyau a kaina.
-
11
Idanuna sun ga fāɗuwar maƙiyana; kunnuwana sun ji kukan mugayen maƙiyana.
-
12
Adalai za su haɓaka kamar itacen dabino, za su yi girma kama al’ul na Lebanon;
-
13
da aka daddasa a gidan Ubangiji, za su haɓaka a filayen gidan Allahnmu.
-
14
Za su ci gaba da ba da ’ya’ya a tsufansu, za su kasance ɗanye kuma kore shar,
-
15
suna shela cewa, “ Ubangiji adali ne; shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa.”