📖 Zabura 91
-
1
Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.
-
2
Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata, Allahna, wanda nake dogara.”
-
3
Tabbatacce zai cece ka daga tarkon mai farauta da kuma daga cututtuka masu kisa.
-
4
Zai rufe ka da fikafikansa, a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka; amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.
-
5
Ba za ka ji tsoron razanar dare, ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,
-
6
ko bala’in da yake aukowa cikin duhu, ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana.
-
7
Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka, dubu goma a hannun damanka, amma ba abin da zai zo kusa da kai.
-
8
Za ka dai gan da idanunka yadda ake hukunta mugaye.
-
9
In ka mai da Mafi Ɗaukaka wurin zamanka, har ma Ubangiji wanda yake mafakata,
-
10
to, babu wani mugun abin da zai same ka, ba masifar da za tă zo kusa da tentinka.
-
11
Gama zai umarci mala’ikunsa game da kai don su tsare ka a dukan hanyoyinka;
-
12
za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.
-
13
Za ka taka zaki da gamsheƙa; za ka tattake babban zaki da maciji.
-
14
Ubangiji ya ce, “Domin ya ƙaunace ni, zan kuɓutar da shi; zan kiyaye shi, gama ya yarda da sunana.
-
15
Zai kira bisa sunana, zan kuma amsa masa; zan kasance tare da shi a lokacin wahala, zan kuɓutar da shi in kuma girmama shi.
-
16
Da tsawon rai zan ƙosar da shi in kuma nuna masa cetona.”