📖 Zabura 9
-
1
Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata; zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka.
-
2
Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka; zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka.
-
3
Abokan gābana sun ja da baya; suka yi tuntuɓe suka hallaka a gabanka.
-
4
Gama ka tabbata da gaskiyata da kuma abin da nake yi; ka zauna a kujerarka, kana yin shari’a da adalci.
-
5
Ka tsawata wa ƙasashe ka kuma hallakar da mugaye; ka shafe sunansu har abada abadin.
-
6
Lalaci marar ƙarewa ya cimma abokan gābanmu, ka tuttumɓuke biranensu; yadda ma ba aka ƙara tunaninsu.
-
7
Ubangiji yana mulki har abada; ya kafa kujerarsa don shari’a.
-
8
Zai hukunta duniya da adalci; zai yi mulkin mutane cikin gaskiya.
-
9
Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya, mafaka a lokutan wahala.
-
10
Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai, gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.
-
11
Rera yabai ga Ubangiji, wanda yake zaune a kursiyi a Sihiyona; yi shela a cikin al’ummai abin da ya aikata.
-
12
Gama shi da yakan ɗauki fansa a kan mai kisa yakan tuna; ba ya ƙyale kukan masu wahala.
-
13
Ya Ubangiji, dubi yadda abokan gābana suna tsananta mini! Ka yi jinƙai ka kuma ɗaga ni daga ƙofofin mutuwa,
-
14
don in furta yabanka cikin ƙofofin ’Yar Sihiyona a can kuwa in yi farin ciki cikin cetonka.
-
15
Al’umma sun fāɗa cikin ramin da suka haƙa wa waɗansu; aka kama ƙafafunsu a ragar da suka ɓoye.
-
16
An san Ubangiji ta wurin gaskiyarsa; an kama mugaye da aikin hannuwansu. Haggayiyon. Sela
-
17
Mugaye za su koma kabari, dukan al’umman da suka manta da Allah.
-
18
Amma har abada ba za a manta da mai bukata ba, ba kuwa sa zuciyar mai wahala zai taɓa hallaka.
-
19
Ka tashi, ya Ubangiji, kada ka bar wani yă yi nasara; bari a hukunta al’ummai a gabanka.
-
20
Ka buge su da rawar jiki, ya Ubangiji; bari al’ummai su sani su mutane ne kurum. Sela