📖 Zabura 89
-
1
Zan rera game da ƙauna mai girma ta Ubangiji har abada; da bakina zan sanar da amincinka a dukan zamanai.
-
2
Zan furta cewa ƙaunarka tana nan daram har abada, cewa ka kafa amincinka a sama kanta.
-
3
Ka ce, “Na yi alkawari da zaɓaɓɓena, na rantse wa Dawuda bawana,
-
4
cewa ‘Zan kafa zuriyarka har abada in kuma sa kursiyinka yă tsaya daram dukan zamanai.’ ” Sela
-
5
Sammai na yabon abubuwan banmamakinka, ya Ubangiji, amincinka shi ma, a cikin taron tsarkakanka.
-
6
Gama wane ne a sarari za a iya kwatanta da Ubangiji? Wane ne yake kamar Ubangiji a cikin talikan samaniya?
-
7
Cikin taron tsarkaka Allah ne aka fi tsoro; shi ne mafi bantsoro fiye da dukan waɗanda suka kewaye shi.
-
8
Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, wane ne kamar ka? Kai mai iko ne, ya Ubangiji, kuma amincinka ya kewaye ka.
-
9
Kana mulkin teku mai tumbatsa; sa’ad da raƙuma sun tashi, kakan kwantar da su.
-
10
Ka ragargaza Rahab kamar waɗanda aka kashe; da hannunka mai ƙarfi ka watsar da abokan gābanka.
-
11
Sammai naka ne, haka kuma duniya; ka kafa duniya da dukan abin da yake cikinta.
-
12
Ka halicce arewa da kudu; Tabor da Hermon suna rera don farin ciki ga sunanka.
-
13
Hannunka mai iko ne; hannunka yana da ƙarfi, hannunka na dama ya sami ɗaukaka.
-
14
Adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinka; ƙauna da aminci suna tafiya a gabanka.
-
15
Masu albarka ne waɗanda suka koyi yin maka kirari waɗanda suke tafiya cikin hasken da yake gabanka, Ubangiji.
-
16
Suna farin ciki a cikin sunanka dukan yini; suna samun ɗaukaka cikin adalcinka.
-
17
Gama kai ne ɗaukakarsu da ƙarfinsu, kuma ta wurin alherinka ka ɗaukaka ƙahonka.
-
18
Tabbatacce, garkuwarmu ta Ubangiji ce, ta sarkinmu ce, da kuma ta Mai Tsarki na Isra’ila ce.
-
19
Ka taɓa yin magana cikin wahayi, ga mutanenka masu aminci ka ce, “Na ba wa jarumi ƙarfi; na ɗaukaka saurayi daga cikin mutane.
-
20
Na sami Dawuda bawana; da mai na mai tsarki na shafe shi.
-
21
Hannuna zai kasance tare da shi; tabbatacce hannuna zai ƙarfafa shi.
-
22
Babu abokin gāban da zai sa yă biya haraji; babu mugun mutumin da zai danne shi.
-
23
Zan murƙushe maƙiyansa a gabansa in kashe dukan abokan gābansa.
-
24
Amintacciya ƙaunata za tă kasance tare da shi, kuma ta wurin sunana za a ɗaukaka ƙahonsa.
-
25
Zan sa hannunsa a bisa teku, hannunsa na dama a bisa koguna.
-
26
Zai yi kira gare ni yă ce, ‘Kai ne Mahaifina, Allahna, Dutse mai cetona.’
-
27
Zan kuma naɗa shi ɗan farina, mafi ɗaukaka cikin sarakunan duniya.
-
28
Zan ci gaba da ƙaunarsa har abada, alkawarina da shi ba zai taɓa fasa ba.
-
29
Zan kafa zuriyarsa har abada, kursiyinsa muddin sammai suna nan.
-
30
“In ’ya’yansa maza suka yashe dokata ba su kuwa bi ƙa’idodina ba,
-
31
in suka take ƙa’idodina suka kuma kāsa kiyaye umarnaina,
-
32
zan hukunta zunubinsu da sanda, laifinsu da bulala;
-
33
amma ba zan ɗauke ƙaunata daga gare shi ba, ba kuwa zan taɓa rasa cika amincina ba.
-
34
Ba zan take alkawarina ba ko in canja abin da leɓunana suka ambata.
-
35
Sau ɗaya ba ƙari, na rantse da tsarkina, ba kuwa zan yi ƙarya wa Dawuda ba,
-
36
cewa zuriyarsa za tă ci gaba har abada kuma kursiyinsa zai dawwama a gabana kamar rana;
-
37
zai kahu har abada kamar wata, amintacciyar shaida a cikin sarari.” Sela
-
38
Amma ka ƙi, ka yi ƙyama ka kuma yi fushi sosai da shafaffenka.
-
39
Ka soke alkawarin da ka yi da bawanka ka kuma ƙazantar da rawaninsa a ƙura.
-
40
Ka rurrushe dukan katangansa ka sa kagaransa suka zama kufai.
-
41
Dukan waɗanda suka wuce sun washe shi; ya zama abin dariya wajen maƙwabtansa.
-
42
Ka ɗaukaka hannun dama na maƙiyansa; ka sa dukan abokan gābansa suna farin ciki.
-
43
Ka juye bakin takobinsa ba ka kuma taimake shi a cikin yaƙi ba.
-
44
Ka kawo ƙarshen darajarsa ka kuma jefar da kursiyinsa ƙasa.
-
45
Ka rage kwanakin ƙuruciyarsa; ka rufe shi da mayafin kunya. Sela
-
46
Har yaushe, ya Ubangiji za ka ɓoye? Za ka ɓoye har abada ne? Har yaushe fushinka zai yi ta ci kamar wuta?
-
47
Ka tuna yadda raina mai wucewa ne. Gama ka halicce dukan mutane ba amfani!
-
48
Wanda mutum ne zai rayu da ba zai ga mutuwa ba, ko yă cece kansa daga ikon kabari? Sela
-
49
Ya Ubangiji, ina ƙaunar mai girma ta dā, wadda cikin amincinka ka rantse wa Dawuda?
-
50
Ka tuna, Ubangiji, yadda aka yi wa bawanka ba’a, yadda na jimre a zuciyata da zage-zagen dukan al’ummai,
-
51
zage-zagen da abokan gābanka suka yi mini, ya Ubangiji, da suka yi wa kowane matakin da shafaffenka ya ɗauka.
-
52
Yabo ya tabbata ga Ubangiji har abada! Amin kuma Amin.