📖 Zabura 88
-
1
Ya Ubangiji, Allah wanda ya cece ni, dare da rana ina kuka a gabanka.
-
2
Bari addu’ata ta zo a gabanka; ka kasa kunne ga kukata.
-
3
Gama raina yana cike da wahala rayuwata tana gab da kabari.
-
4
An lissafta ni cikin waɗanda suka gangara zuwa cikin rami; ni kamar mutumin da ba shi da ƙarfi ne.
-
5
An ware ni tare da matattu, kamar waɗanda aka kashe da suke kwance a kabari, waɗanda ba ka ƙara tunawa, waɗanda aka yanke daga taimakonka.
-
6
Ka sa ni a ramin da yake can ƙasa cikin zurfafa mafi duhu.
-
7
Hasalarka tana da nauyi a kaina; ka turmushe ni da dukan raƙumanka. Sela
-
8
Ka ɗauke abokaina na kurkusa daga gare ni ka sa na zama abin ƙyama a gare su. An kange ni, ba yadda zan kuɓuta
-
9
idanuna ba sa gani sosai saboda baƙin ciki. Ina kira gare ka, ya Ubangiji, kowace rana; na tā da hannuwana zuwa gare ka.
-
10
Kakan nuna wa matattu ayyukanka na banmamaki ne? Waɗanda suka mutu sukan tashi su yabe ka ne? Sela
-
11
Ana furta ƙaunar a cikin kabari ne, ana zancen amincinka a cikin Hallaka ne?
-
12
An san ayyukanka masu banmamaki a wurin duhu ne, ko ayyukan adalcinka a lahira?
-
13
Amma ina kuka gare ka neman taimako, ya Ubangiji; da safe addu’ata kan zo gabanka.
-
14
Don me, ya Ubangiji, ka ƙi ni ka kuma ɓoye fuskarka daga gare ni?
-
15
Tun ina ƙarami na sha wahala na kuma yi kusa in mutu; na sha wahalar razanarka kuma na kuma fid da zuciya.
-
16
Hasalarka ta sha kaina; razanarka ta hallaka ni.
-
17
Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa; sun mamaye ni ɗungum.
-
18
Ka ɗauke abokaina da ƙaunatattuna daga gare ni; duhu ne abokina na kurkusa.