📖 Zabura 85
-
1
Ka nuna wa ƙasarka alheri, ya Ubangiji; ka mai da nasarorin Yaƙub.
-
2
Ka gafarta laifin mutanenka ka kuma shafe dukan zunubansu. Sela
-
3
Ka kau da dukan fushinka ka kuma juye daga hasalar fushinka.
-
4
Ka sāke mai da mu, ya Allah Mai Cetonmu, ka kau da rashin jin daɗinka daga gare mu.
-
5
Za ka ci gaba da fushi da mu har abada ne? Za ka ja fushinka cikin dukan tsararraki?
-
6
Ba za ka sāke raya mu ba, don mutanenka su yi farin ciki a cikinka?
-
7
Ka nuna mana ƙaunarka marar ƙarewa, ya Ubangiji, ka kuma ba mu cetonka.
-
8
Zan saurari abin da Allah Ubangiji zai faɗa; ya yi alkawarin salama ga mutanensa, tsarkakansa, amma kada su koma ga wauta.
-
9
Tabbatacce cetonsa yana kusa da waɗanda suke tsoronsa, don ɗaukakarsa ta zauna a cikin ƙasarmu.
-
10
Ƙauna da aminci za su sadu; adalci da salama za su yi wa juna sumba.
-
11
Aminci zai ɓulɓulo daga ƙasa, adalci kuma yă duba daga sama.
-
12
Ubangiji tabbatacce zai bayar da abin da yake da kyau, ƙasarmu kuwa za tă ba da amfaninta.
-
13
Adalci na tafiya a gabansa yana shirya hanya domin ƙafafunsa.