📖 Zabura 83
-
1
Ya Allah, kada ka yi shiru; kada ka tsaya cik, ya Allah, kada ka daina motsi.
-
2
Dubi yadda abokan gābanka suke fariya, dubi yadda maƙiyanka suke ɗaga kansu.
-
3
Da wayo suna ƙulle-ƙulle a kan mutanenka; suna shirya maƙarƙashiya a kan waɗanda kake so.
-
4
Suna cewa, “Ku zo, bari mu hallaka su ɗungum a matsayin al’umma, don kada a ƙara tuna da sunan Isra’ila.”
-
5
Da zuciya ɗaya suka yi ƙulle-ƙulle tare; suka haɗa kai gāba da kai,
-
6
tentunan Edom da na mutanen Ishmayel, na Mowab da kuma na Hagirawa,
-
7
Gebal, Ammon da Amalek, Filistiya, tare da mutanen Taya.
-
8
Har Assuriya ma ta haɗa kai da su don ta ba da ƙarfi ga zuriyar Lot. Sela
-
9
Ka yi musu abin da ka yi wa Midiyan, yadda ka yi wa Sisera da Yabin a kogin Kishon,
-
10
waɗanda suka hallaka a En Dor suka zama kamar juji a ƙasa.
-
11
Ka mai da manyansu kamar Oreb da Zeyib, dukan sarakunansu kamar Zeba da Zalmunna,
-
12
waɗanda suka ce, “Bari mu mallaki wuraren kiwon Allah.”
-
13
Ka mai da su kamar ɗan tsiron da kan karye, iska ta yi ta turawa, ya Allahna, kamar yayin da iska take hurawa,
-
14
kamar yadda wuta ke cin kurmi ko harshen wutar da take ci a kan duwatsu,
-
15
haka za ka kore su da iska mai ƙarfi ka kuma firgita su da guguwarka.
-
16
Ka rushe fuskokinsu da kunya don mutane su nemi sunanka, ya Ubangiji.
-
17
Bari su kasance cikin kunya da taƙaici; bari su hallaka cikin wulaƙanci.
-
18
Bari su san cewa kai, wanda sunansa ne Ubangiji, cewa kai kaɗai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya.