📖 Zabura 82
-
1
Allah yana shugabanta cikin babban taro; yakan zartar da hukunci a cikin “alloli”.
-
2
“Har yaushe za ku kāre marasa adalci ku kuma goyi bayan mugaye? Sela
-
3
Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu; ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya.
-
4
Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata; ku kuɓutar da su daga hannun mugaye.
-
5
“Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba. Suna yawo cikin duhu; an girgiza dukan tussan duniya.
-
6
“Na ce, ‘Ku “alloli” ne; dukanku ’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ ne.
-
7
Amma za ku mutu kamar mutum kurum; za ku fāɗi kamar duk wani mai mulki.”
-
8
Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya, gama dukan al’ummai gādonka ne.