📖 Zabura 80
-
1
Ka ji mu, ya Makiyayin Isra’ila, kai da ka bishe Yusuf kamar garke. Kai da kake zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, ka haskaka
-
2
a gaban Efraim, Benyamin da Manasse. Ka tā da ƙarfinka; ka zo ka cece mu.
-
3
Ka mai da mu, ya Allah; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu kuwa cetu.
-
4
Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, har yaushe fushinka zai yi ta ƙuna a kan addu’o’in mutanenka?
-
5
Ka ciyar da su da burodin hawaye; ka sa suka sha hawaye ta cikakken kwaf.
-
6
Ka mai da mu abin faɗa ga maƙwabtanmu, kuma abokan gābanmu suna mana ba’a.
-
7
Ka mai da mu, ya Allah Maɗaukaki; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu za mu kuwa cetu.
-
8
Ka fitar da inabi daga Masar; ka kori al’ummai ka kuma dasa shi.
-
9
Ka gyara wuri saboda shi, ya kuwa yi saiwa ya cike ƙasa.
-
10
Aka rufe duwatsu da inuwarsa, manya-manyan itatuwan al’ul da rassansa.
-
11
Ya miƙe rassansa zuwa Teku tohonsa har zuwa Kogi.
-
12
Me ya sa ka rurrushe bangayensa don duk masu wucewa su tsinke ’ya’yan inabinsa?
-
13
Aladu daga kurmi suna ɓarnatar da shi halittun gonaki kuma suna cinsa.
-
14
Ka komo wurinmu, ya Allah Maɗaukaki! Ka duba daga sama ka gani! Ka lura da wannan inabi,
-
15
saiwar da hannun damarka ya dasa, ɗan da ka renar wa kanka.
-
16
An yanke inabinka, an ƙone shi da wuta; a tsawatawarka mutanenka sun hallaka.
-
17
Bari hannunka yă zauna a kan mutumin da yake hannun damarka, ɗan mutum da ka renar wa kanka.
-
18
Ta haka ba za mu juye mu bar ka ba; ka rayar da mu, za mu kuwa kira bisa sunanka.
-
19
Ka mai da mu, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu kuwa cetu.