📖 Zabura 8
-
1
Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya! Ka kafa ɗaukakarka bisa sammai.
-
2
Daga leɓunan yara da jarirai ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka da masu ɗaukan fansa su yi shiru.
-
3
Sa’ad da na dubi sammai, aikin yatsotsinka, wata da taurari waɗanda ka ajiye a wurarensu,
-
4
wane ne mutum da kake tunawa da shi, ɗan mutum da kake lura da shi?
-
5
Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.
-
6
Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka; ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa,
-
7
dukan shanu da tumaki, da kuma namun jeji,
-
8
tsuntsayen sararin sama da kifin teku, da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku.
-
9
Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya!