3abin da muka ji muka kuma sani, abubuwan da kakanninmu suka faɗa mana.
4Ba za mu ɓoye su wa ’ya’yanmu ba; za mu faɗa wa tsara mai zuwa ayyukan da suka zama yabo na Ubangiji, ikonsa, da abubuwan banmamakin da ya aikata.
5Ya kafa ƙa’idodi wa Yaƙub ya kuma kafa doka a cikin Isra’ila, wadda ya umarce kakanni-kakanninmu su koya wa ’ya’yansu,
6don tsara na biye su san su, har da ’ya’yan da ba a riga an haifa ba, su kuma su faɗa wa ’ya’yansu.
7Ta haka za su dogara ga Allah ba kuwa za su manta da ayyukansa ba amma za su kiyaye umarnansa.
8Ba za su zama kamar kakanni kakanninsu ba, masu taurinkai da kuma tsara masu tayarwa, waɗanda zukatansu ba su yi biyayya ga Allah ba, waɗanda zukatansu ba su yi aminci ga Allah ba.
9Mutanen Efraim, ko da yake suna da bakkuna, suka juya da baya a ranar yaƙi;
10ba su kiyaye alkawarin Allah ba suka kuma ƙi su yi rayuwa ta wurin dokarsa.
11Suka manta da abin da ya aikata, abubuwan banmamakin da ya nuna musu.
12Ya yi mu’ujizai a idanun kakanninsu a ƙasar Masar, a yankin Zowan.
13Ya raba teku ya kuma bi da su ciki; ya sa ruwa ya tsaya daram kamar bango.
14Ya bishe su da girgije da rana da kuma haske daga wuta dukan dare.
15Ya tsage duwatsu a cikin hamada ya kuma ba su ruwaye a yalwace kamar tekuna;
16ya fid da rafuffuka daga dutsen da ya tsaga ya sa ruwa ya gudu kamar koguna.
17Amma suka ci gaba da yin masa zunubi, suna tayarwa a cikin hamada a kan Mafi Ɗaukaka.
18Da gangan suka gwada Allah ta wurin neman abincin da suke kwaɗayi.
19Suka yi magana a kan Allah, suna cewa, “Allah zai iya shimfiɗa tebur a cikin hamada?
20Sa’ad da ya bugi dutse, ruwa ya ɓulɓulo, rafuffuka suka yi gudu a yalwace. Amma zai iya ba mu abinci? Zai iya tanada wa mutanensa nama?”
21Sa’ad da Ubangiji ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; wutarsa ta ɓarke a kan Yaƙub, hasalarsa kuwa ta tashi a kan Isra’ila,
22gama ba su gaskata ga Allah ba ko su dogara ga cetonsa.
23Duk da haka ya ba da umarni ga sarari a bisa ya kuma buɗe ƙofofin sammai;
24ya sauko da Manna wa mutanensa don su ci, ya ba su hatsin sama.
25Mutane suka ci burodin mala’iku; ya aika musu dukan abincin da za su iya ci.
26Ya saki iskar gabas daga sammai ya kuma saki iskar yamma ta wurin ikonsa.
27Ya sauko da nama a kansu kamar ƙura, tsuntsaye masu firiya kamar yashi a bakin teku.
28Ya sa suka sauka a cikin sansaninsu, ko’ina kewaye da tentunansu.
29Suka ci har suka sami fiye da abin da ya ishe su, gama ya ba su abin da suka yi kwaɗayi.
30Amma kafin su juyo daga abincin da suka yi kwaɗayi, kai tun ma yana a bakunansu,
31fushin Allah ya ƙuna a kansu; ya karkashe waɗanda suka fi ƙiba a cikinsu, yana yankan matasan Isra’ila.
32Duk da haka, suka ci gaba da yin zunubi; duk da abubuwan banmamakinsa, ba su gaskata ba.
33Saboda haka ya sa kwanakinsu suka ƙare a banza shekarunsu kuma cikin masifa.
34A duk sa’ad da Allah ya kashe su, sai su neme shi; sukan juyo a natse gare shi.
35Sun tuna cewa Allah ne Dutsensu, cewa Allah Mafi Ɗaukaka ne Mai fansarsu.
36Amma sai su yi ta yin masa zaƙin baki, suna masa ƙarya da harsunansu;
37zukatansu ba sa biyayya gare shi, ba su da aminci ga alkawarinsa.
38Duk da haka ya kasance mai jinƙai; ya gafarta laifofinsu bai kuwa hallaka su ba. Sau da sau ya janye fushinsa bai kuwa sa fushinsa yă ƙuna ba.
39Ya tuna cewa su naman jiki ne kawai, iska mai wucewa da ba ta dawowa.
40Sau da yawa sun tayar masa a cikin hamada suka kuma ɓata masa rai a jeji!
41Sau da sau suka riƙa gwada Allah; suka tsokane Mai Tsarki na Isra’ila.
42Ba su tuna da ikonsa, a ranar da ya fanshe su daga mai danniya,
43ranar da ya nuna mu’ujizansa a Masar abubuwan banmamakinsa a yankin Zowan ba.
44Ya mai da kogunansu suka zama jini; ba su iya sha daga rafuffuka ba.
45Ya aika da tarin ƙudajen da suka cinye su, da kwaɗin da suka wahalshe su.
46Ya ba da hatsinsu ga fāra, amfanin gonakinsu ga ɗango.
47Ya lalace inabinsu da ƙanƙara itatuwan al’ul nasu kuma da jaura.
48Ya miƙa shanunsu ga ƙanƙara, tumakinsu ga aradun tsawa.
49Ya saki musu fushinsa mai zafi, hasalarsa, zafin rai da kuma ɓacin ransa, ƙungiyar mala’iku masu hallakarwa.
50Ya shirya hanya wa fushinsa; bai tsare ransu daga mutuwa ba amma ya miƙa su ga annoba.
51Ya bugi kowane ɗan fari na Masar, mafari ƙarfin mazantakansu a tentunan Ham.
52Amma ya fitar da mutanensa kamar garke; ya bi da su kamar tumaki ta cikin hamada.
53Ya bi da su lafiya ƙalau, don kada su ji tsoro; amma teku ya cinye abokan gābansu.
54Ta haka ya kawo su iyakar ƙasa mai tsarki, zuwa ƙasar tudun da hannunsa na dama ya kame.
55Ya kori al’ummai a gabansu ya rarraba ƙasashensu gare su a matsayin gādo; ya zaunar da kabilan Isra’ila a gidajensu.
56Amma suka gwada Allah suka tayar wa Mafi Ɗaukaka; ba su kiyaye ƙa’idodinsa ba.