📖 Zabura 77
-
1
Na yi kuka ga Allah don taimako; na yi kuka ga Allah don yă ji ni.
-
2
Sa’ad da nake cikin damuwa, na nemi Ubangiji; da dare na miƙa hannuwa ba gajiya raina kuma ya ƙi yă ta’azantu.
-
3
Na tuna da kai, ya Allah, na kuma yi nishi; na yi nishi, ƙarfina kuwa duk ya raunana. Sela
-
4
ka hana idanuna rufewa; na damu ƙwarai har ba na iya magana.
-
5
Na yi tunani kwanakin da suka wuce, shekarun da suka wuce da daɗewa;
-
6
na tuna da waƙoƙina da dare. Zuciyata ta yi nishi, ƙarfina kuwa ya nemi yă sani.
-
7
“Ubangiji zai ƙi ne har abada? Ba zai taɓa nuna alherinsa kuma ba?
-
8
Ƙaunarsa marar ƙarewa ta ɓace ke nan har abada? Alkawarinsa ya kāsa ke nan a dukan lokaci?
-
9
Allah ya manta yă yi jinƙai? Cikin fushinsa ya janye tausayinsa ne?” Sela
-
10
Sai na yi tunani, “Zan yi roƙo saboda wannan, shekarun da Mafi Ɗaukaka ya miƙa hannunsa na dama.”
-
11
Zan tuna da ayyukan Ubangiji; I, zan tuna mu’ujizanka na tun dā.
-
12
Zan yi tunani a kan dukan ayyukanka in lura da dukan manyan abubuwan da ka aikata.
-
13
Hanyoyinka, ya Allah, masu tsarki ne. Wanda allah ne yake da girma kamar Allahnmu?
-
14
Kai ne Allahn da yakan aikata mu’ujizai; ka nuna ikonka a cikin mutane.
-
15
Da hannunka mai ƙarfi ka fanshi mutanenka, zuriyar Yaƙub da Yusuf. Sela
-
16
Ruwaye sun gan ka, ya Allah, ruwaye sun gan ka suka firgita; zurfafan gaske sun girgiza.
-
17
Gizagizai sun sauko da ruwa, sararin sama suka buga tsawa; kibiyoyinka suka yi ta kai komo da walƙiya.
-
18
Aka ji tsawanka a cikin guguwa, walƙiyarka ta haskaka duniya; duniya ta yi rawar jiki ta girgiza.
-
19
Hanyarka ta bi ta cikin teku, hanyarka ta bi cikin manyan ruwaye, duk da haka ba a ga sawunka ba.
-
20
Ka bi da mutanenka kamar garke ta hannun Musa da Haruna.