📖 Zabura 76
-
1
A cikin Yahuda an san Allah; sunansa da girma yake a cikin Isra’ila.
-
2
Tentinsa yana a Salem mazauninsa yana a Sihiyona.
-
3
A can ya kakkarya kibiyoyin wuta, garkuwoyi da takuban, makaman yaƙi. Sela
-
4
Darajarka tana da haske, fiye da darajar tuddai waɗanda suke cike da namun jeji masu yawa.
-
5
Jarumawa sun zube kamar ganima sun yi barcinsu na ƙarshe; ba ko jarumi guda da zai iya ɗaga hannuwansa.
-
6
A tsawatawarka, ya Allah na Yaƙub, doki da keken yaƙi suka kwanta ba motsi.
-
7
Kai kaɗai ne za a ji tsoro. Wane ne zai iya tsayawa sa’ad da ka yi fushi?
-
8
Daga sama ka yi shelar hukunci, ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit,
-
9
sa’ad da kai, ya Allah, ka tashi don ka yi shari’a, don ka cece dukan masu shan wahala a ƙasar. Sela
-
10
Tabbatacce fushinka a kan mutane kan jawo maka yabo, waɗanda suka tsira daga fushinka za su zama kamar rawaninka.
-
11
Ku yi alkawari wa Ubangiji Allahnku ku kuma cika su; bari dukan ƙasashen maƙwabta su kawo kyautai ga Wannan da za a ji tsoro.
-
12
Ya kakkarya ƙarfin masu mulki; sarakunan duniya suna tsoronsa.