📖 Zabura 75
-
1
Muna maka godiya, ya Allah, muna maka godiya, gama Sunanka yana kusa; mutane na faɗin ayyukanka masu banmamaki.
-
2
Ka ce, “Na zaɓi ƙayyadadden lokaci; ni ne wanda yake shari’ar gaskiya.
-
3
Sa’ad da duniya da dukan mutanenta suka girgiza, ni ne wanda na riƙe ginshiƙan daram. Sela
-
4
Ga masu girman kai na ce, ‘Kada ku ƙara taƙama,’ ga mugaye kuma, ‘Kada ku ɗaga ƙahoninku.
-
5
Kada ku ɗaga ƙahoninku gāba da sama; kada ku yi magana da miƙaƙƙen wuya.’ ”
-
6
Ba wani daga gabas ko yamma ko hamada da zai ɗaukaka mutum.
-
7
Amma Allah ne mai yin shari’a, yakan saukar da wannan, yă kuma tayar da wani.
-
8
A hannun Ubangiji akwai kwaf cike da ruwan inabi mai kumfa gauraye da kayan yaji; yakan zuba shi, dukan mugayen duniya kuwa su sha shi tas.
-
9
Game da ni dai, zan furta wannan har abada; zan rera yabo ga Allah na Yaƙub,
-
10
wanda ya ce, “Zan yanke ƙahonin dukan mugaye, amma za a ɗaga ƙahonin adalai sama.”