📖 Zabura 71
-
1
A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka; kada ka taɓa sa in sha kunya.
-
2
Ka kuɓutar da ni ka cece ni cikin adalcinka; ka juya kunnenka gare ni ka kuma cece ni.
-
3
Ka zama dutsena da kagarata, inda kullum zan je. Ka ba da umarni a cece ni, gama kai ne dutsen ɓuyana da katangata.
-
4
Ka cece ni, ya Allahna, daga hannun mugaye, da kuma daga ikon mugaye da masu mugunta.
-
5
Gama kai ne abin sa zuciyata, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ƙarfin zuciyata tun ina yaro.
-
6
Daga haihuwa na dogara gare ka; kai ka kawo ni daga cikin mahaifiyata. Kullayaumi zan yabe ka.
-
7
Na zama kamar abin sa zuciya ga yawanci, amma kai ne katangata mai ƙarfi.
-
8
Bakina ya cika da yabonka, ina furta darajarka dukan yini.
-
9
Kada ka yar da ni sa’ad da na tsufa; kada ka yashe ni sa’ad da ƙarfina ya ƙare.
-
10
Gama abokan gābana suna magana a kaina; waɗanda suke jira su kashe ni suna haɗa baki tare.
-
11
Suna cewa, “Allah ya yashe shi; mu fafare shi mu kama shi, gama ba wanda zai kuɓutar da shi.”
-
12
Kada ka yi nisa da ni, ya Allah; zo da sauri, ya Allahna, ka taimake ni.
-
13
Bari masu zagina su hallaka da kunya; bari waɗanda suke so su cutar da ni su sha ba’a da kuma kunya.
-
14
Amma game da ni, kullayaumi zan kasance da sa zuciya; zan yabe ka sau da sau.
-
15
Bakina zai ba da labarin adalcinka, zai yi maganar cetonka dukan yini, ko da yake ban san yawansa ba.
-
16
Zan zo in furta in kuma yi shelar ayyukanka masu girma, ya Ubangiji Mai Iko Duka; zan yi shelar adalcinka, naka kaɗai.
-
17
Tun ina yaro, ya Allah, ka koya mini har wa yau ina furta ayyukanka masu banmamaki.
-
18
Ko sa’ad da na tsufa da furfura, kada ka yashe ni, ya Allah, sai na furta ikonka ga tsara mai zuwa, ƙarfinka ga dukan waɗanda suke zuwa.
-
19
Adalcinka ya kai sararin sama, ya Allah, kai da ka yi manyan abubuwa. Wane ne kamar ka, ya Allah?
-
20
Ko da yake ka sa na ga wahaloli, masu yawa da kuma masu ɗaci, za ka sāke mayar mini da rai; daga zurfafan duniya za ka sāke tā da ni.
-
21
Za ka ƙara girmana ka sāke ta’azantar da ni.
-
22
Zan yabe ka da garaya saboda amincinka, ya Allah; zan rera yabo gare ka da molo, Ya Mai Tsarki na Isra’ila.
-
23
Leɓunana za su yi sowa don farin ciki sa’ad da na rera yabo gare ka, ni, wanda ka fansa.
-
24
Harshena zai ba da labarin ayyukanka masu adalci dukan yini, gama waɗanda suka so su cutar da ni sun sha kunya suka kuma rikice.