1Ka hanzarta, ya Allah, ka cece ni; Ya Ubangiji, zo da sauri ka taimake ni.
2Bari masu neman raina su sha kunya su kuma rikice; bari dukan masu sha’awar gani lalacewata su juye baya da kunya.
3Bari masu ce mini, “Allah yă ƙara!” Su juye baya saboda kunyansu.
4Amma bari dukan masu nemanka su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka; bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce, “Bari Allah yă sami ɗaukaka!”
5Duk da haka ni matalauci ne da kuma mai bukata; ka zo da sauri gare ni, ya Allah. Kai ne mai taimakona da mai cetona; Ya Ubangiji, kada ka yi jinkiri.