📖 Zabura 7
-
1
Ya Ubangiji Allahna, na zo neman mafaka a wurinka; ka cece ni ka kuɓutar da ni daga dukan waɗanda suke bi na,
-
2
in ba haka ba za su yayyage ni kamar zaki su ɓarke ni kucu-kucu ba tare da wani da zai cece ni ba.
-
3
Ya Ubangiji Allahna, in na yi kuskure aka kuwa sami laifi a hannuwana,
-
4
in na yi mugunta ga wanda yake zaman lafiya da ni ko kuwa ba da wani dalilin cuci abokin gābana,
-
5
to, bari abokin gābana yă bi yă kuma cim mini; bari yă tattake raina a ƙasa ya sa in kwana a ƙura. Sela
-
6
Ka tashi, ya Ubangiji, cikin fushinka; ka tashi gāba da fushin abokan gābana. Ka farka, Allahna, ka umarta adalci.
-
7
Bari taron mutane su taru kewaye da kai. Ka yi mulki a bisansu daga bisa;
-
8
bari Ubangiji mai shari’ar mutane. Ka shari’anta ni Ya Ubangiji, bisa ga adalcina, bisa ga mutuncina, ya Mafi Ɗaukaka.
-
9
Ya Allah mai adalci, wanda yake binciken tunani da zukata, ka kawo ƙarshen rikicin mugaye ka kuma sa adalai su zauna lafiya.
-
10
Garkuwata shi ne Allah Mafi Ɗaukaka, wanda yake ceton masu tsabtar zuciya.
-
11
Allah alƙali ne mai adalci, Allahn da yakan bayyana fushinsa kowace rana.
-
12
In mutum bai tuba ba, Allah zai wasa takobinsa; zai tanƙware yă kuma ɗaura bakansa.
-
13
Ya shirya makamansa masu dafi; ya shirya kibiyoyinsa masu wuta.
-
14
Wanda yake da cikin mugunta ya kuma ɗauki cikin damuwa yakan haifi ƙarya.
-
15
Wanda ya haƙa rami yakan fāɗa cikin ramin da ya haƙa.
-
16
Damuwar da ya ja yakan sāke nannaɗe a kansa; fitinarsa takan sauka a kansa.
-
17
Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa zan kuma rera yabo ga sunan Ubangiji Mafi Ɗaukaka.