2Na nutse cikin laka mai zurfi, inda babu wurin tsayawa. Na shiga cikin ruwaye masu zurfi; rigyawa ya sha kaina.
3Na gaji da kira ina neman taimako; maƙogwarona ya bushe idanuna sun dushe, suna neman Allahna.
4Waɗanda suke ƙina ba dalili sun fi gashin kaina yawa; da yawa ne abokan gābana babu dalili, su da suke nema su hallaka ni. An tilasta mini in mayar da abin da ban sata ba.
5Ka san wautata, ya Allah; laifina ba a ɓoye yake daga gare ka ba.
6Bari waɗanda suke sa zuciya gare ka kada su sha kunya saboda ni, Ya Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki; bari waɗanda suke neman ka kada su sha kunya saboda ni, Ya Allah na Isra’ila.
7Gama na jimre da ba’a saboda kai, kunya kuma ta rufe fuskata.
8Ni baƙo ne a cikin ’yan’uwana, bare kuma ga ’ya’yan mahaifiyata maza;
9gama himma da nake yi wa gidanka yana ƙunata, kuma zagi na masu zaginka yana fāɗuwa a kaina.
10Sa’ad da na yi kuka na kuma yi azumi dole in jimre da ba’a;
11sa’ad da na sanya rigunan makoki, mutane suna maishe ni abin dariya.
12Masu zama a ƙofa suna mini ba’a, na zama waƙa a bakin bugaggu da giya.
13Amma na yi addu’a gare ka, ya Ubangiji, a lokacin da ka ga dama; a cikin ƙaunarka mai girma, ya Allah, ka amsa mini da tabbacin ceto.
14Ka fid da ni daga laka, kada ka bari in nutse; ka cece ni daga waɗanda suke ƙina, daga rurin ruwaye.
15Kada ka bar rigyawa yă sha kaina ko zurfafa su haɗiye ni ko rami yă rufe bakinsa a kaina.
16Ka amsa mini, ya Ubangiji cikin alherin ƙaunarka; cikin jinƙanka mai girma ka juyo gare ni.
17Kada ka ɓoye fuskarka daga bawanka; ka amsa mini da sauri, gama ina cikin wahala.
18Ka zo kusa ka kuɓutar da ni; ka fanshe ni saboda maƙiyana.
19Ka san yadda ake mini ba’a, ake kunyatar da ni da kuma yadda nake shan kunya; dukan abokan gābana suna a gabanka.
20Ba’a ta sa zuciyata ta karai ta bar ni ba mataimaki; Na nemi a ji tausayina, amma ban sami ko ɗaya ba, na nemi masu ta’aziyya, amma ban sami ko ɗaya ba.
21Sun sa abin ɗaci cikin abincina suka kuma ba ni ruwan inabi mai tsami sa’ad da nake jin ƙishi.
22Bari teburin da aka shirya a gabansu yă zama musu tarko; bari yă zama sakamakon laifi da kuma tarko.
23Bari idanunsu yă dushe don kada su gani, bayansu kuma yă tanƙware har abada.
24Ka kwarara fushinka a kansu; bari fushinka mai zafi yă ci musu.
25Bari wurinsu yă zama kufai; kada ka bar wani yă zauna a tentunansu.
26Gama sun tsananta wa waɗanda ka hukunta suna kuma taɗin wahalar waɗanda ka ji musu rauni.
27Ka neme su da laifi a kan laifi; kada ka bar su su sami rabo a cikin cetonka.
28Bari a shafe su sarai daga littafin rai kada a kuma lissafta su tare da adalai.
29Ina cikin zafi da kuma azaba; bari cetonka, ya Allah, yă tsare ni.
30Zan yabe sunan Allah cikin waƙa in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya.
31Wannan zai gamshi Ubangiji fiye da saniya, fiye da bijimi da ƙahoninsa da kuma kofatansa.
32Matalauta za su gani su kuma yi murna, ku da kuke neman Allah, bari zukatanku su rayu!
33Ubangiji yakan ji masu bukata ba ya kuwa ƙyale kamammun mutanensa.
34Bari sama da ƙasa su yabe shi, tekuna da dukan abin da yake motsi a cikinsu,
35gama Allah zai cece Sihiyona yă sāke gina biranen Yahuda. Sa’an nan mutane za su zauna a can su mallake ta,
36’ya’yan bayinsa za su gāje ta, waɗanda kuma suna ƙaunar sunansa za su zauna a can.