1Bari Allah yă tashi, bari a watsar da abokan gābansa; bari maƙiyansa su gudu a gabansa.
2Kamar yadda iska take hura hayaƙi, bari yă hura su haka; kamar yadda kaki kan narke a gaban wuta, bari mugaye su hallaka a gaban Allah.
3Amma bari adalai su yi murna su kuma yi farin ciki a gaban Allah; bari su yi murna da farin ciki.
4Rera wa Allah, rera yabo ga sunansa, ku ɗaukaka wanda yake hawa a kan gizagizai; sunansa Ubangiji ne, ku kuma yi farin ciki a gabansa.
5Uba ga marayu, mai kāre gwauraye, shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki.
6Allah ya shirya masu kaɗaici a cikin iyalai, ya jagorance ’yan kurkuku da waƙoƙi; amma ’yan tawaye suna zama a ƙasa mai zafin rana.
7Sa’ad da ka fito a gaban mutanenka, ya Allah, sa’ad da ka taka ta cikin ƙasar da take wofi, Sela
8duniya ta girgiza, sammai suka zuba ruwan sama, a gaban Allah, wanda ya bayyana a Sinai, a gaban Allah, Allah na Isra’ila.
9Ka ba da yayyafi a yalwace, ya Allah; ka rayar da gādonka da ya gāji.
10Mutanenka suka zauna a cikinsa, kuma daga yalwarka, ya Allah, ka tanada wa matalauta.
11Ubangiji ya yi umarni, mutane masu yawa ne suka yi shelarsa,
12“Sarakuna da mayaƙa suka gudu a gaggauce; cikin sansani mutane sun raba ganima.
13Har yayinda kuke barci a cikin garken tumaki, an dalaye fikafikan kurciya da azurfa, fikafikanta da zinariya mai ƙyalli.”
14Sa’ad da Maɗaukaki ya watsar da sarakuna a cikin ƙasa, sai ya zama kamar ƙanƙara ta sauka a kan Zalmon.
15Duwatsun Bashan, duwatsu masu alfarma ne; duwatsun Bashan masu wuyar hawa ne.
16Don me kuke duba da kishi, ya duwatsu masu wuyan hawa, a kan dutsen da Allah ya zaɓa yă yi mulki, inda Ubangiji kansa zai zauna har abada?
17Karusan Allah ninkin dubbai goma ne da kuma dubu dubbai; Ubangiji ya zo daga Sinai ya shiga cikin haikalinsa.
18Sa’ad da ka hau bisa, ka bi da kamammu cikin tawagarka; ka karɓi kyautai daga mutane, har ma daga ’yan tawaye, don kai, ya Ubangiji Allah, za ka zauna a can.
19Yabo ya tabbata ga Ubangiji, ga Allah Mai Cetonmu, wanda kullum yake ɗaukan nauyinmu. Sela
20Allahnmu shi ne Allah wanda yake ceto; daga Ubangiji Mai Iko Duka kuɓuta yake zuwa daga mutuwa.
21Tabbatacce Allah zai murƙushe kawunan abokan gābansa, rawanin gashi na waɗanda suke ci gaba cikin zunubansa.
22Ubangiji ya ce, “Zan kawo su daga Bashan; zan kawo su daga zurfafan teku,
23don ku wanke ƙafafunku a cikin jinin maƙiyanku, yayinda harsunan karnukanku su sami rabonsu.”
24Jerin gwanonka ya zo a bayyane, ya Allah, jerin gwanon Allahna da Sarkina zuwa cikin wuri mai tsarki.
25A gaba akwai mawaƙa, a bayansu akwai makaɗa; tare da su akwai ’yan mata suna bugan ganguna.
26Ku yabi Allah cikin taro mai girma; yabi Ubangiji cikin taron Isra’ila.
27Ga ƙaramar kabilar Benyamin, suna jagorance su, ga babbar ƙungiya shugabannin Yahuda, ga kuma shugabannin Zebulun da na Naftali.
28Ka bayyana ikonka, ya Allah; ka nuna ƙarfinka, ya Allah, kamar yadda ka yi a dā.
29Saboda haikalinka a Urushalima sarakuna za su kawo maka kyautai.
30Ka tsawata wa naman jejin nan a cikin kyauro, garken bijimai a cikin ’yan maruƙan al’ummai. Ka ƙasƙantar, bari yă kawo sandunan azurfa. Ka watsar da al’ummai waɗanda suke jin daɗin yaƙi.
31Jakadu za su zo daga Masar; Kush za tă miƙa kanta ga Allah.
32Ku rera wa Allah, ya masarautan duniya, ku rera yabo ga Ubangiji, Sela
33gare shi wanda yake hawan daɗaɗɗen sararin sama, wanda yake tsawa da babbar murya.
34Ku yi shelar ikon Allah, wanda ɗaukakarsa take a bisa Isra’ila, wanda ikonsa yake a cikin sarari.
35Kai mai banmamaki ne, ya Allah, cikin wurinka mai tsarki; Allah na Isra’ila yakan ba da iko da kuma ƙarfi ga mutanensa. Yabo ya tabbata ga Allah!