📖 Zabura 67
-
1
Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu, Sela
-
2
don a san hanyoyinka a duniya, cetonka kuma a cikin dukan al’ummai.
-
3
Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe ka.
-
4
Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki, gama kana mulkin mutanenka da adalci kana kuma bi da al’umman duniya. Sela
-
5
Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe.
-
6
Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbinta Allah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu.
-
7
Allah yă sa mana albarka, dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.