📖 Zabura 66
-
1
Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah, dukan duniya!
-
2
Ku rera ɗaukaka ga sunansa; ku sa yabonsa yă zama da ɗaukaka!
-
3
Ku ce wa Allah, “Ayyukanka da banmamaki suke! Ikonka da girma yake har abokan gābanka suna durƙusa a gabanka.
-
4
Dukan duniya sun rusuna a gabanka suna rera yabo gare ka, suna rera yabo ga sunanka.” Sela
-
5
Ku zo ku ga abin da Allah ya yi, ayyukansa masu banmamaki a madadin mutum!
-
6
Ya juya teku zuwa busasshiyar ƙasa, sun wuce cikin ruwaye da ƙafa, ku zo, mu yi farin ciki a cikinsa.
-
7
Yana mulki har abada ta wurin ikonsa, idanunsa suna duban al’ummai, kada ’yan tawaye su tayar masa. Sela
-
8
Ku yabi Allahnku, ya mutane, bari a ji ƙarar yabonsa;
-
9
ya adana rayukanmu ya kuma kiyaye ƙafafunmu daga santsi.
-
10
Gama kai, ya Allah, ka gwada mu; ka tace mu kamar azurfa.
-
11
Ka kawo mu cikin kurkuku ka kuma jibga kaya masu nauyi a bayanmu.
-
12
Ka bar mutane suka hau a kawunanmu; mun bi ta wuta da ruwa, amma ka kawo mu zuwa wurin yalwa.
-
13
Zan zo haikalinka da hadayun ƙonawa zan kuwa cika alkawurana gare ka,
-
14
alkawuran da leɓunana suka yi alkawari bakina kuma ya faɗa sa’ad da nake cikin wahala.
-
15
Zan miƙa kitsen dabbobi gare ka da kuma baye-baye na raguna; zan miƙa bijimai da awaki. Sela
-
16
Ku zo ku saurara, dukanku waɗanda suke tsoron Allah; bari in faɗa muku abin da ya yi mini.
-
17
Na yi kuka gare shi da bakina; yabonsa yana a harshena.
-
18
Da a ce na ji daɗin zunubi a zuciyata, da Ubangiji ba zai saurara ba;
-
19
amma tabbatacce Allah ya saurara ya kuma ji muryata a cikin addu’a.
-
20
Yabo ga Allah, wanda bai ƙi addu’ata ba ko yă janye ƙaunarsa daga gare ni!