1Yabo ya dace da kai, ya Allah, a Sihiyona; a gare ka za mu cika alkawuranmu
2Ya kai wanda yake jin addu’a a gare ka dukan mutane za su zo.
3Sa’ad da zunubai suka sha ƙarfinmu, ka gafarta laifofinmu.
4Masu albarka ne waɗanda ka zaɓa ka kawo kusa don su zauna a filayenka! Mun cika da abubuwa masu kyau na gidanka, na haikalinka mai tsarki.
5Ka amsa mana da ayyuka masu banmamaki na adalci, Ya Allah Mai Cetonmu, begen dukan iyakar duniya da kuma na tekuna masu nesa,
6wanda ya yi duwatsu ta wurin ikonka, bayan ka kintsa kanka da ƙarfi,
7wanda ya kwantar da rurin tekuna, rurin raƙumansu, da kuma tumbatsar al’ummai.
8Waɗanda suke zama can da nesa sukan ji tsoron manyan ayyukanka; inda safe ke haskaka yamma kuma ta shuɗe kakan sa a yi waƙoƙin farin ciki.
9Kana kula da ƙasa kana kuma yi mata banruwa; kana azurta ta a yalwace. Rafuffukan Allah sun cika da ruwa don su ba mutane hatsi, don haka ne ka ƙaddara.
10Ka kwarara ta da ruwa ka kuma baje kunyoyinta; ka sa ta yi laushi da yayyafi ka kuma albarkaci tsire-tsirenta.
11Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka, amalankenka kuwa sun cika har suna zuba.
12Makiyayan hamada sun cika har suna zuba; tuddai sun rufu da murna.
13Wurin dausayin kiwo sun rufu da garkuna kwari kuma sun cika da hatsi; suna sowa don farin ciki.