📖 Zabura 63
-
1
Ya Allah, kai ne Allahna, da nacewa na neme ka; raina yana ƙishinka, jikina yana marmarinka, cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye inda babu ruwa.
-
2
Na gan ka a wuri mai tsarki na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka.
-
3
Domin ƙaunarka ta fi rai kyau, leɓunana za su ɗaukaka ka.
-
4
Zan yabe ka muddin raina, kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana.
-
5
Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau; da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka.
-
6
A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare.
-
7
Domin kai ne mai taimakona, ina rera a cikin inuwar fikafikanka.
-
8
Raina ya manne maka; hannunka na dama yana riƙe da ni.
-
9
Su da suke neman raina za su hallaka; za su gangara zuwa zurfafan duniya.
-
10
Za a bayar da su ga takobi su kuma zama abincin karnukan jeji.
-
11
Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah; dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi, amma za a rufe bakunan maƙaryata.