1Raina na samun hutu a wurin Allah ne kaɗai; cetona na zuwa daga gare shi.
2Shi kaɗai ne dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.
3Har yaushe za ku tasar wa mutum guda? Dukanku ne za ku kā da shi wannan jinganannen bango, wannan rusasshen katanga?
4Sun kintsa sosai su tumɓuke shi daga matsayinsa mai martaba; suna jin daɗi yin ƙarairayi. Sukan sa wa mutum albarka da bakinsu, amma a zuciyarsu la’antawa suke yi. Sela
5Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai; dogarata kan zo daga gare shi ne.
6Shi ne kaɗai dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.
7Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne, shi ne dutsena mai ƙarfi, mafakata.
8Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane; ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi, gama Allah ne mafakarmu. Sela
9Talakawa dai kamar shaƙar iska suke, Attajirai dai kamar shirim suke; in aka auna a ma’auni, su ba wani abu ba ne; dukansu dai kamar shaƙar iska ne kawai.
10Kada ku dogara a kan ƙwace ko yin fariya a kayan sata; ko arzikinku ya ƙaru, kada ku sa zuciyarku a kansu.
11Abu guda Allah ya ce, abubuwa biyu na ji, “Cewa kai, ya Allah, kake mai ƙarfi,
12kuma cewa kai, ya Ubangiji, mai ƙauna ne. Tabbatacce za ka sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya yi.”