📖 Zabura 61
-
1
Ka ji kukata, ya Allah; ka saurari addu’ata.
-
2
Daga iyakar duniya na yi kira gare ka, na yi kira yayinda zuciyata ta karai; ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi.
-
3
Gama kai ne mafakata, hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi.
-
4
Ina marmari in zauna a tentinka har abada in sami mafaka a cikin inuwar fikafikanka. Sela
-
5
Gama ka ji alkawarina, ya Allah; ka ba ni gādo na waɗanda suke tsoron sunanka.
-
6
Ka ƙara kwanakin ran sarki, shekarunsa su kasance a zamanai masu yawa.
-
7
Bari yă yi mulki a gaban Allah har abada; ka sa ƙaunarka da amincinka su tsare shi.
-
8
Sa’an nan zan riƙa rera yabo ga sunanka in kuma cika alkawarina kowace rana.