📖 Zabura 60
-
1
Ka ki mu, ya Allah, ka kuma fashe kāriyarmu; ka yi fushi da mu, yanzu ka mai da mu!
-
2
Ka girgiza ƙasar ka kuma tsaga ta; ka daure karayarta, gama tana rawa.
-
3
Ka nuna wa mutanenka lokutan wahala; ka ba mu ruwan inabin da ya sa muka bugu.
-
4
Amma ga waɗanda suke tsoronka, ka ɗaga tuta don a buɗe gāba da baka. Sela
-
5
Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama, domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta.
-
6
Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki, “Da nasara zan rarraba Shekem in kuma auna Kwarin Sukkot.
-
7
Gileyad nawa ne, Manasse kuma nawa ne; Efraim shi ne hular kwanona, Yahuda kuma sandar mulkina.
-
8
Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirarin nasara.”
-
9
Wa zai kawo ni birnin katanga? Wa zai bishe ni zuwa Edom?
-
10
Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?
-
11
Ka ba mu gudummawa a kan abokin gāba, gama taimakon mutum banza ne.
-
12
Tare da Allah za mu yi nasara, zai kuma tattake abokan gābanmu.