📖 Zabura 6
-
1
Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka ko ka hore ni cikin hasalarka.
-
2
Ka yi mini jinƙai, Ubangiji, gama na suma; Ya Ubangiji, ka warkar da ni, gama ƙasusuwana suna zafin ciwo.
-
3
Raina yana cikin wahala. Har yaushe, ya Ubangiji, har yaushe?
-
4
Ka juyo, ya Ubangiji, ka cece ni; ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka.
-
5
Babu wanda yakan tuna da kai sa’ad da ya mutu. Wa ke yabonka daga kabari?
-
6
Na gaji tiƙis daga nishi. Dukan dare na jiƙe gadona da kuka na jiƙe kujerata da hawaye.
-
7
Idanuna sun rasa ƙarfi da baƙin ciki; sun rasa ƙarfi saboda dukan abokan gābana.
-
8
Ku tafi daga gare ni, dukanku masu aikata mugunta, gama Ubangiji ya ji kukata.
-
9
Ubangiji ya ji kukata saboda jinƙansa; Ubangiji ya karɓi addu’ata.
-
10
Dukan abokan gābana za su sha kunya su kuma karaya; za su juya da kunya nan da nan.