📖 Zabura 59
-
1
Ka cece ni daga abokan gābana, ya Allah; ka tsare ni daga waɗanda suka tayar mini.
-
2
Ka kuɓutar da ni daga masu aikata mugunta ka kuma cece ni daga masu kisa.
-
3
Duba yadda suka kwanta suna jirana! Mugaye suna ƙulle-ƙullen gāba da ni ba saboda wani dalili ko na yi wa wani zunubi ba, ya Ubangiji.
-
4
Ban yi wani laifi ba, duk da haka suna a shirye su fāɗa mini. Tashi ka taimake ni; dubi halin da nake ciki!
-
5
Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, ka tashi ka hukunta dukan al’ummai; kada ka nuna jinƙai ga mugaye maciya amana. Sela
-
6
Sukan dawo da yamma, suna wage haƙora kamar karnuka, suna yawo a birni.
-
7
Dubi abin da suke tofawa daga bakunansu, suna tofar da takuba daga leɓunansu, suna cewa, “Wa zai ji mu?”
-
8
Amma kai, ya Ubangiji, kakan yi musu dariya; kana yi wa dukan waɗannan al’ummai ba’a.
-
9
Ya ƙarfina, na dogara gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata,
-
10
Allah mai ƙaunata. Allah zai sha gabana zai kuma sa in yi dariya a kan waɗanda suke magana marar kyau a kaina.
-
11
Amma kada ka kashe su, ya Ubangiji garkuwarmu, in ba haka mutanena za su manta. Cikin ikonka ka sa su yi ta yawo barkatai, ka kuma kawar da su.
-
12
Saboda zunuban bakunansu, saboda maganganun leɓunansu, bari a kama su cikin fariyarsu. Saboda zage-zage da ƙarairayin da suke yi,
-
13
ka cinye su da hasala, ka cinye su sarai. Sa’an nan za a sani a iyakar duniya cewa Allah yana mulki a bisa Yaƙub. Sela
-
14
Sukan dawo da yamma, suna wage haƙora kamar karnuka, suna yawo a birni.
-
15
Suna ta yawo neman abinci su kuwa yi haushi in ba su ƙoshi ba.
-
16
Amma zan rera game da ƙarfinka, da safe zan rera game da ƙaunarka; gama kai ne mafakata, kagarata a lokacin wahala.
-
17
Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata, Allah mai ƙaunata.