📖 Zabura 56
-
1
Ka yi mini jinƙai, ya Allah, gama mutane sun tasar mini da zafi; dukan yini suna matsa harinsu.
-
2
Masu ɓata sunana suna bina dukan yini; da yawa suna kai mini hari cikin fariyarsu.
-
3
Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka.
-
4
Ga Allah wanda maganarsa nake yabo ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba. Me mutum mai mutuwa zai yi mini?
-
5
Dukan yini sun yi ta juya maganata; kullum suna ƙulle-ƙulle su cuce ni.
-
6
Sun haɗa baki, sun ɓoye, suna kallon takawata suna a shirye su ɗauki raina.
-
7
Sam, kada ka bari su kuɓuce; cikin fushinka, ya Allah, ka saukar da al’ummai.
-
8
Ka lissafta makokina; ka jera hawayena a littafinka, ba a rubuce suke a cikin littafinka ba?
-
9
Ta haka abokan gābana za su juya da baya sa’ad da na nemi taimako. Ta haka zan san cewa Allah yana tare da ni.
-
10
Ga Allah, wanda nake yabon maganarsa, ga Ubangiji, wanda nake yabon maganarsa,
-
11
ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?
-
12
Ina ƙarƙashin alkawari gare ka, ya Allah; zan miƙa hadayuna na godiya gare ka.
-
13
Gama ka cece ni daga mutuwa da kuma ƙafafun daga tuntuɓe, don in yi tafiya a gaban Allah cikin hasken rai.