2ka ji ni ka kuma amsa mini. Tunanina yana damuna na kuma gaji tilis
3hankalina ya tashi saboda yawan surutan masu ƙina, saboda danniyar mugaye. Gama sukan jawo mini wahala, suna jin haushina suna ƙina.
4Zuciyata tana wahala a cikina; tsorace-tsoracen mutuwa sun sha kaina.
5Tsoro da rawan jiki sun kama ni; razana ta sha kaina.
6Na ce, “Kash, da a ce ina da fikafikan kurciya mana! Ai, da na yi firiya na tafi na huta,
7da na tafi can da nisa na zauna a hamada; Sela
8da na hanzarta na tafi wurin mafakata, nesa da muguwar iska da hadiri.”
9Ka rikitar da mugaye, ya Ubangiji, ka birkitar da maganarsu, gama na ga rikici da faɗa a cikin birni.
10Dare da rana suna yawo a kan katanga; mugun hali da zargi suna a cikinta.
11Rundunar hallaka suna aiki a cikin birni; barazana da ƙarairayi ba sa taɓa barin titunanta.
12Da a ce abokin gāba ne ke zagina, da na jure da shi; da a ce maƙiyi yana tā da kansa a kaina, da na ɓoye daga gare shi.
13Amma kai ne, mutum kamar ni, abokina, abokina na kurkusa,
14wanda na taɓa jin daɗin zumunci da shi sosai yayinda muke tafiya tare a taron jama’a a gidan Allah.
15Bari mutuwa ta ɗauki abokan gābana ba labari; bari su gangara da rai zuwa cikin kabari, gama mugunta tana samun masauƙi a cikinsu.
16Amma na kira ga Allah, Ubangiji kuwa ya cece ni.
17Safe, rana da yamma ina kuka da nishi, yakan kuwa ji muryata.
18Yakan fisshe ni lafiya daga yaƙin da ake yi da ni, ko da yake da yawa suna gāba da ni.
19Allah, yana mulki har abada, zai ji su yă kuma azabtar da su, Sela mutanen da ba sa taɓa canja hanyoyinsu kuma ba sa tsoron Allah.
20Abokina ya kai wa abokansa hari; ya tā da alkawarinsa.
21Maganarsa tana da laushi kamar man zaitun, duk da haka yaƙi yana a cikin zuciyarsa; kalmominsa sun fi mai sulɓi, duk da haka takuba ne zārarru.
22Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji zai kuwa riƙe ku; ba zai taɓa barin mai adalci yă fāɗi ba.
23Amma kai, ya Allah, za ka kawar da mugaye zuwa cikin ramin lalacewa; masu kisa da mutane masu ruɗu ba za su kai rabin kwanakin rayuwarsu ba. Amma ni dai, na dogara gare ka.