📖 Zabura 54
-
1
Ka cece ni, ya Allah ta wurin sunanka; ka nuna ni marar laifi ne ta wurin ƙarfinka.
-
2
Ka ji addu’ata, ya Allah; ka saurari maganar bakina.
-
3
Baƙi suna kawo mini hari; mutane marasa imani suna neman raina, mutanen da ba sa tsoron Allah. Sela
-
4
Tabbatacce Allah ne mai taimakona, Ubangiji shi ne wanda yake riƙe ni.
-
5
Bari mugunta ta shaƙe masu magana marar kyau a kaina; cikin amincinka ka hallaka su.
-
6
Zan miƙa hadaya ta yardar rai gare ka; zan yabe sunanka, ya Ubangiji, gama yana da kyau.
-
7
Gama ya cece ni daga dukan wahalolina, idanuna kuma sun ga an yi nasara a kan maƙiyana.