📖 Zabura 52
-
1
Me ya sa kake fariya game da mugunta, kai babban mutum? Me ya sa kake fariya dukan yini, kai da kake abin kunya a idanun Allah?
-
2
Harshenka kan shirya hallaka; yana nan kamar reza mai ci, kana ta ruɗu.
-
3
Kana ƙaunar mugunta fiye da alheri, ƙarya a maimakon faɗin gaskiya. Sela
-
4
Kana ƙaunar kowace kalmar cutarwa, Ya kai harshe mai ruɗu!
-
5
Tabbatacce Allah zai kai ka ga madawwamiyar hallaka. Zai fizge ka yă yayyage ka daga tentinka; zai tumɓuke ka daga ƙasar masu rai. Sela
-
6
Masu adalci za su ga su ji tsoro; za su yi masa dariya, suna cewa,
-
7
“Yanzu, ga mutumin da bai mai da Allah mafakarsa ba amma ya dogara a yawan arzikinsa ya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!”
-
8
Amma ni kamar itace zaitun ne ina haɓaka a gidan Allah; na dogara ga ƙauna marar ƙarewa ta Allah har abada abadin.
-
9
Zan yabe ka har abada game da abin da ka yi; a cikin sunanka zan dogara, gama sunanka yana da kyau. Zan yabe ka a gaban tsarkakanka.