1Ka yi mini jinƙai, ya Allah, bisa ga ƙaunarka marar ƙarewa; bisa ga tausayinka mai girma ka shafe laifofina.
2Ka wanke dukan kurakuraina ka tsarkake ni daga zunubina.
3Gama ina sane da laifofina zunubaina kuma kullum suna a gabana.
4Kai kaɗai na yi wa zunubi na yi abin da yake mugu a idonka, ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta.
5Tabbatacce ni mai zunubi ne tun haihuwa mai zunubi daga lokacin da mahaifiyata ta yi cikina.
6Tabbatacce kana son gaskiya a sassan ciki; ka koya mini hikima a wuri can ciki.
7Ka tsarkake ni da hizzob, zan kuwa zama tsab; ka wanke ni, zan kuma fi dusan ƙanƙara fari.
8Bari in ji farin ciki da murna; bari ƙasusuwan da ka ragargaza su yi farin ciki.
9Ka ɓoye fuskarka daga zunubaina ka kuma shafe dukan kurakuraina.
10Ka halitta zuciya mai tsabta a cikina, ya Allah, ka kuma sabunta tsayayyen ruhu a cikina.
11Kada ka fid da ni daga gabanka ko ka ɗauke Ruhunka Mai Tsarki daga gare ni.
12Ka mayar mini farin cikin cetonka ka kuma ba ni ruhun biyayya, yă riƙe ni.
13Ta haka zan koyar wa masu laifi hanyoyinka, masu zunubi kuma za su komo gare ka.
14Ka cece ni daga laifin jini, ya Allah, Allahn da ya cece ni, harshena kuwa zai rera adalcinka.
15Ya Ubangiji, ka buɗe leɓunana, bakina kuwa zai furta yabonka.
16Ba ka farin ciki a hadaya, ai da na kawo; ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa.
17Hadayun Allah su ne karyayyen ruhu; karyayyiya da kuma zuciya mai tuba, Ya Allah, ba za ka ƙi ba.
18Cikin jin daɗinka ka sa Sihiyona ta yi nasara; ka gina katangar Urushalima.
19Ta haka za a kasance da hadayu masu adalci, hadayun ƙonawa ɗungum don su faranta ka; sa’an nan za a miƙa bijimai a bagadenka.