📖 Zabura 50
-
1
Maɗaukaki, Allah, Ubangiji, ya yi magana ya kuma kira duniya daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa.
-
2
Daga Sihiyona, cikakkiya a kyau, Allah na haskakawa.
-
3
Allahnmu yana zuwa ba kuwa zai yi shiru ba; wuta mai cinyewa a gabansa, babban hadari kuma ya kewaye shi.
-
4
Ya kira sammai da suke bisa, da duniya, don yă shari’anta mutanensa.
-
5
“Ku tattara mini shafaffuna, waɗanda suka yi alkawari da ni ta wurin hadaya.”
-
6
Sammai kuwa sun yi shelar adalcinsa gama Allah kansa alƙali ne. Sela
-
7
“Ku ji, ya mutanena, zan kuwa yi magana, Ya Isra’ila, zan kuwa ba da shaida a kanku. Ni ne Allah, Allahnku.
-
8
Ba na tsawata muku saboda hadayunku ko kuwa hadayunku na ƙonawa, waɗanda kuka taɓa kawo a gabana.
-
9
Ba na bukatan bijimi daga turkenku ko awaki daga garkunanku,
-
10
gama kowace dabbar kurmi nawa ne, da kuma shanu a kan dubban tuddai.
-
11
Na san kowane tsuntsun da yake a duwatsu kuma halittun filaye nawa ne.
-
12
Da a ce ina jin yunwa ai, ba sai na faɗa muku ba, gama duniyar nawa ne, da kome da yake cikinta.
-
13
Ina cin naman bijimai ne ko ina shan jinin awaki ne?
-
14
“Ku miƙa hadayar godiya ga Allah, ku cika alkawuranku ga Mafi Ɗaukaka,
-
15
ku kira gare ni a ranar wahala; zan cece ku, za ku kuwa girmama ni.”
-
16
¶ Amma ga mugaye, Allah ya ce, “Wace dama ce kuke da ita na haddace dokokina ko na yin maganar alkawarina a leɓunanku?
-
17
Kun ƙi umarnina kuka kuma zubar da kalmomina a bayanku
-
18
Sa’ad da kuka ga ɓarawo, kukan haɗa kai da shi; kukan haɗa kai da mazinata.
-
19
Kuna amfani da bakunanku don mugunta kuna kuma gyara harshenku don ruɗu.
-
20
Kuna ci gaba da magana a kan ɗan’uwanku ku kuma yi maganar ƙarya a kan ɗan mahaifinku.
-
21
Kun yi waɗannan abubuwa na kuwa yi shiru; kun ɗauka gaba ɗaya ni kamar ku ne. Amma zan tsawata muku in kuma zarge ku a fuskarku.
-
22
“Ku lura da wannan, ku da kuka manta da Allah, ko kuwa in yayyage ku kucu-kucu, ba kuma wanda zai cece ku.
-
23
Shi wanda ya miƙa hadayun godiya yakan girmama ni, ya kuma shirya hanya saboda in nuna masa ceton Allah.”