1Ku ji wannan, dukanku mutane; ku saurara, dukanku waɗanda suke zama a wannan duniya,
2babba da yaro mai arziki da talaka.
3Bakina zai yi maganar hikima; magana daga zuciyata za tă ba da ganewa.
4Zan juye kunnena ga karin magana; da garaya zan ƙarfafa kacici-kacicina.
5Don me zan ji tsoro sa’ad da mugayen kwanaki suka zo, sa’ad da mugaye masu ruɗu suka kewaye ni,
6waɗanda suka dogara ga arzikinsu suna kuma fariya a kan yawan arzikinsu?
7Ba wani da zai iya ceton ran wani ko yă ba wa Allah kuɗin fansa saboda shi,
8kuɗin fansa domin rai yana da tsada, babu abin da za a biya da ya taɓa isa,
9da zai sa yă ci gaba da rayuwa har abada yă hana shi shigan kabari yă ruɓa.
10Gama kowa na iya ganin masu hikima na mutuwa; wawaye da marasa azanci su ma kan hallaka su bar wa waɗansu arzikinsu.
11Kaburburansu za su ci gaba da zama gidajensu har abada, Can za su kasance har zamanai marasa ƙarewa, ko da yake sun ba wa filaye sunayen kansu.
12Amma mutum, kome arzikinsa, ba ya dawwama; shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.
13Wannan ne ƙaddarar waɗanda suke dogara a kansu, da kuma ta mabiyansu, waɗanda suka tabbatar da faɗinsu. Sela
14Kamar tumaki an ƙaddara su ga kabari; za su kuwa zama abincin mutuwa amma masu gaskiya za su yi mulki a kansu da safe. Kamanninsu za su ruɓe a cikin kabari, nesa da gidajensu masu tsada.
15Amma Allah zai ceci raina daga kabari; tabbatacce zai ɗauke ni zuwa wurinsa. Sela
16Kada ka razana da yawa sa’ad da mutum ya yi arziki sa’ad da darajar gidansa ta ƙaru;
17gama ba zai ɗauki kome tare da shi sa’ad da ya mutu ba, darajarsa ba za tă gangara tare da shi ba.
18Ko da yake yayinda yake a raye ya ɗauka kansa mai albarka ne, mutane kuma sun yabe ka sa’ad da kake cin nasara,
19zai gamu da tsarar kakanninsa, waɗanda ba za su taɓa ganin hasken rayuwa ba.
20Mutumin da yake da arziki ba tare da ganewa ba shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.