📖 Zabura 48
-
1
Ubangiji mai girma ne, kuma mafificin yabo, a birnin Allahnmu, dutsensa mai tsarki.
-
2
Kyakkyawa ce cikin tsayinta, abin farin cikin dukan duniya. Kamar ƙwanƙoli mafi tsayi na Zafon ne Dutsen Sihiyona, birnin Babban Sarki.
-
3
Allah yana cikin fadodinta; ya nuna kansa mafaka ce gare ta.
-
4
Sa’ad da sarakuna suka haɗa rundunoni, sa’ad da suka yi gaba tare,
-
5
sun gan ta suka kuwa yi mamaki; suka gudu don tsoro.
-
6
Rawar jiki ya kama su a can, zafi kamar na mace mai naƙuda.
-
7
Ka hallaka su kamar jiragen ruwan Tarshish da iskar gabas ta wargaje.
-
8
Yadda muka ji, haka muka gani a cikin birnin Ubangiji Maɗaukaki, a cikin birnin Allahnmu. Allah ya sa ta zauna lafiya har abada. Sela
-
9
Cikin haikalinka, ya Allah, mun yi tunani a kan ƙaunarka marar ƙarewa.
-
10
Kamar sunanka, ya Allah, yabonka ya kai iyakokin duniya; hannunka na dama ya cika da adalci.
-
11
Dutsen Sihiyona ya yi farin ciki, ƙauyukan Yahuda suna murna saboda hukuntanka.
-
12
Yi tafiya cikin Sihiyona, ku kewaye ta, ku ƙirga hasumiyoyinta,
-
13
ku lura da katangarta da kyau, ku dubi fadodinta, don ku faɗe su ga tsara mai zuwa.
-
14
Gama wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin; zai zama jagorarmu har zuwa ƙarshe.