📖 Zabura 47
-
1
Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai; ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki.
-
2
Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne, Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya!
-
3
Ya rinjayi al’ummai a ƙarƙashinmu, mutane kuma a ƙarƙashin ƙafafunmu.
-
4
Ya zaɓar mana gādonmu, abar taƙamar Yaƙub, wanda yake ƙauna. Sela
-
5
Allah ya haura a cikin sowa ta farin ciki, Ubangiji ya haura a cikin ƙarar ƙahoni.
-
6
Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai; ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai.
-
7
Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya; ku rera zabura ta yabo gare shi.
-
8
Allah yana mulki a bisa al’ummai; Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki.
-
9
Manyan mutanen al’ummai sun taru a matsayin mutanen Allah na Ibrahim, gama sarkunan duniya na Allah ne; ana ɗaukaka shi ƙwarai.