📖 Zabura 46
-
1
Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.
-
2
Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,
-
3
ko da ruwansa suna ruri suna kumfa duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. Sela
-
4
Akwai kogi mai rafuffukan da suke sa birnin Allah murna, tsattsarkan wuri inda Mafi Ɗaukaka ke zama.
-
5
Allah yana cikinta, ba za tă fāɗi ba; Allah zai taimake ta da safe.
-
6
Al’ummai suna hayaniya, mulkoki sun fāɗi; ya ɗaga muryarsa, duniya ta narke.
-
7
Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela
-
8
Zo ku ga ayyukan Ubangiji, kangon da ya kawo a kan duniya.
-
9
Ya sa yaƙoƙi suka yi tsit ko’ina a duniya. Ya kakkarya bakkuna ya kuma ragargaza māsu, ya ƙone garkuwoyi da wuta.
-
10
“Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah; za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai, za a ɗaukaka ni cikin duniya.”
-
11
Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela