1Zuciyata ta cika da kyakkyawan kan magana yayinda nake rera ayoyina wa sarki; harshena ne alƙalamin ƙwararren marubuci.
2Kai ne mafi kyau cikin mutane an kuma shafe leɓunanka da alheri, da yake Allah ya albarkace ka har abada.
3Ka ɗaura takobinka a gefenka, ya jarumi; ka rufe kanka da ɗaukaka da kuma daraja.
4Cikin darajarka ka hau zuwa nasara a madadin gaskiya, tawali’u da adalci; bari hannunka na dama yă nuna ayyukan banmamaki.
5Bari kibiyoyinka masu tsini su huda zukatan abokan gāban sarki; bari al’ummai su fāɗi ƙarƙashin ƙafafunka.
6Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin; sandar adalci zai zama sandar mulkinka.
7Kana ƙaunar abin da yake daidai kana kuma ƙin mugunta; saboda haka Allah, Allahnka, ya sa ka a bisa abokanka ta wurin shafe ka da man farin ciki.
8Dukan rigunanka suna ƙanshin turaren mur da na aloyes, da na kashiya; daga kowace fadan da aka yi masa ado da hauren giwa kaɗe-kaɗen tsirkiya kan sa ka murna.
9’Ya’yan sarki mata suna cikin matan da ake girmama; a hannun damarka kuwa ga amarya, sarauniya saye da ofir zinariya.
10Ki saurara, ya ke diya, ki lura ku kuma kasa kunne, Ki manta da mutanenki da gidan mahaifinki.
11Sarki ya cika da sha’awar kyanki; ki girmama shi, gama shi ne maigidanki.
12Diyar Taya za tă zo da kyauta, mawadata za su nemi tagomashinki.
13Gimbiya tana fada, kyakkyawa ce ainun; an saƙa rigarta da zaren zinariya.
14Cikin riguna masu ado aka kai ta wurin sarki; abokanta budurwai suna biye da ita aka kuwa kawo su gare ka.
15Aka bi da su cikin farin ciki da murna; suka shiga fadan sarki.
16’Ya’yanka maza za su maye matsayin kakanninka; za ka sa su yi mulki a duk fāɗin ƙasar.
17Zan sa a tuna da kai a dukan zamanai; saboda haka al’ummai za su yabe ka har abada abadin.