📖 Zabura 41
-
1
Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi; Ubangiji yakan kuɓutar da shi a lokutan wahala.
-
2
Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa; zai albarkace shi a cikin ƙasar ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba.
-
3
Ubangiji zai ba shi ƙarfi a gadon rashin lafiyarsa ya mayar masa da lafiya daga ciwon da ya kwantar da shi.
-
4
Na ce, “Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai; ka warkar da ni, gama na yi maka zunubi.”
-
5
Abokan gābana suna muguwar magana a kaina cewa, “Yaushe zai mutu sunansa yă ɓace ne?”
-
6
Duk sa’ad da wani ya zo ganina, yakan yi maganar ƙarya, yayinda zuciyarsa tana tattare da cin zarafi; sa’an nan yă fita yă yi ta bazawa ko’ina.
-
7
Dukan abokan gābana suna raɗa tare a kaina; suna fata mugun abu ya same ni, suna cewa,
-
8
“Mugun ciwo ya kama shi; ba zai taɓa tashi daga inda yake kwanciya ba.”
-
9
Har abokina na kurkusa, wanda na amince da shi, wanda muke cin abinci tare, ya juya yana gāba da ni.
-
10
Amma kai, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai, ka tā da ni, don in sāka musu.
-
11
Na sani kana jin daɗina, gama abokin gābana ba zai ci nasara a kaina ba.
-
12
Cikin mutuncina ka riƙe ni ka sa ni a gabanka har abada.
-
13
Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, har abada abadin. Amin kuma Amin.