📖 Zabura 38
-
1
Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka ko ka hore ni cikin hasalarka.
-
2
Gama kibiyoyinka sun soke ni, hannunka kuma ya fāɗo a kaina.
-
3
Saboda hasalarka babu lafiya a jikina; ƙasusuwana ba lafiya saboda zunubina.
-
4
Laifofina sun mamaye ni kamar nauyin da ya sha ƙarfin ɗauka.
-
5
Miyakuna sun ruɓe suna kuma wari saboda wawancina na zunubi.
-
6
An tanƙware ni aka kuma ƙasƙantar da ni; dukan yini ina ta kuka.
-
7
Bayana yana fama da zazzaɓi; babu lafiya a jikina.
-
8
Na gaji sharkaf an kuma ragargaza ni; ina nishi da wahala a cikin zuciyata.
-
9
Dukan bukatata tana a shimfiɗe a gabanka, ya Ubangiji; ajiyar zuciyata ba ta ɓoyuwa daga gare ka.
-
10
Zuciyata na bugu, ƙarfina kuma ya ƙare, har ma haske ya rabu da idanuna.
-
11
Abokaina da maƙwabtana sun guje ni saboda miyakuna; maƙwabtana ba sa zuwa kusa.
-
12
Waɗanda suke neman raina sun sa tarkonsu, waɗanda suke so su cuce ni suna zance lalatar da ni; yini sukutum suna ƙulla mini maƙarƙashiya.
-
13
Ni kamar kurma ne, wanda ba ya ji, kamar bebe, wanda ba ya iya buɗe bakinsa.
-
14
Na zama kamar mutumin da ba ya ji, wanda bakinsa ba ya iya ba da amsa.
-
15
Na dogara gare ka, ya Ubangiji; za ka amsa, ya Ubangiji Allahna.
-
16
Gama na ce, “Kada ka bar su su yi farin ciki a kaina ko su yi kirari a kaina sa’ad da ƙafata ta yi santsi.”
-
17
Gama ina gab da fāɗuwa, kuma cikin azaba nake kullum.
-
18
Na furta laifina; na damu da zunubina.
-
19
Da yawa ne masu gāba da ni da ƙarfi; waɗanda suke kina ba dalili sun yi yawa.
-
20
Waɗanda suke sāka alherina da mugunta, suna cin zarafina sa’ad da nake bin abin da yake daidai.
-
21
Ya Ubangiji, kada ka yashe ni; kada ka yi nesa da ni, ya Allahna.
-
22
Zo da sauri ka taimake ni, Ya Ubangiji Mai Cetona.